Kwanan nan ne majalisar gudanarwar kasar Sin, ta amince da ranar 19 ga watan Agusta a matsayin ranar likitocin kasar Sin. Hukumar lafiya da kayyade iyali ta kasa da sassan da ke da alaka da su ne za su gudanar da wannan aiki, inda za a gudanar da bikin ranar likitocin kasar Sin karo na farko a shekara mai zuwa.

Ranar Likitocin kasar Sin ita ce ranar kwararru ta hudu a kasar Sin, bayan ranar ma'aikatan jinya, da ranar malamai da na 'yan jarida, wanda ke nuna muhimmancin likitocin wajen kiyaye lafiyar jama'a.

A ranar 19 ga watan Agusta ne za a gudanar da bikin ranar likitocin kasar Sin, saboda an gudanar da taron tsaftar muhalli da kiwon lafiya na farko a sabon karni a nan birnin Beijing a ranar 19 ga watan Agustan shekarar 2016. Taron ya kasance wani muhimmin ci gaba a fannin kiwon lafiya a kasar Sin.

A gun taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi karin haske kan muhimmin matsayi na aikin tsafta da kiwon lafiya a dukkan al'amuran jam'iyyar da kuma manufofin kasar, tare da gabatar da ka'idoji kan aikin tsafta da kiwon lafiya na kasar a sabon zamani.

Kafa ranar Likitoci na da matukar amfani wajen daukaka martabar likitoci a idon jama’a, kuma hakan zai taimaka wajen kyautata alaka tsakanin likitoci da marasa lafiya.


Lokacin aikawa: Agusta-19-2022